Friday, 31 January 2020

Da misalin karfe goma na safiyar yau Juma’a Kwamared Nura Aliyu Batsari ya zanta da manema labarai a dai dai kofar shiga birnin Katsina domin fara tattakin da ya yi wa kansa alkawarin yi zuwa Kano
Wannan Tattaki na da nufin taya gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje murnar nasarar da ya samu a kotun Koli dangane da shari’ar da suka gabza da dan takarar jam’iyyar PDP Injiya Abba Kabir (Abba Gida Gida)

Acikin jawabin kwamared Nura Batsari ya shaidawa manema labarai cewa ya shirya wannan tafiya ne saboda kishin da yake da shi ga jam’iiyarsu ta APC kuma ita ce ta yi nasara a wannan kara da aka fafata tsakanin mutane biyu inda daga karshen gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya samu nasara.
A gobe asabar idan Allah ya kaimu ake sa ran matashin zai tashi daga Kankia zuwa garin Tsanyawa ta jihar Kano, a garin Tsanyawa zai samu tarba daga shugabannin jam’iyyar  Apc na karamar hukumar Tsanyawa, bayan sun gaisa zai wuce karamar hukumar Bichi da ke cikin jihar Kano, inda zai yada zango a  Garin Bichi.
Haka kuma ana sa ran cewa Nura Aliyu Batsari zai samu tarba daga shugabannin jam’iyyar Apc na karamar hukumar Bichi, sannan zai kai gaisuwa ga Mai Martaba Sarkin Bichi Alhaji Aminu Ado Bayero.
Kazalika idan Allah ya kaimu lahadi da safe  zai wuce zuwa cikin garin Kano fadar Gwamnatin jihar Kano, inda zai sadu Mai girma Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya gabatar da jawabin shi na taya murna.
Wannan tattaki dai kamar yadda ya fada, yana a matsayin girmamawa ne daga ‘ya ‘yan jam’iyyar APC ta jihar Katsina zuwa ga gwamna Abdullahi Umar Ganduje da kuma al’ummar jihar Kano baki daya

No comments:

Post a Comment