Friday, 31 January 2020

Da misalin karfe goma na safiyar yau Juma’a Kwamared Nura Aliyu Batsari ya zanta da manema labarai a dai dai kofar shiga birnin Katsina domin fara tattakin da ya yi wa kansa alkawarin yi zuwa Kano
Wannan Tattaki na da nufin taya gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje murnar nasarar da ya samu a kotun Koli dangane da shari’ar da suka gabza da dan takarar jam’iyyar PDP Injiya Abba Kabir (Abba Gida Gida)

Acikin jawabin kwamared Nura Batsari ya shaidawa manema labarai cewa ya shirya wannan tafiya ne saboda kishin da yake da shi ga jam’iiyarsu ta APC kuma ita ce ta yi nasara a wannan kara da aka fafata tsakanin mutane biyu inda daga karshen gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya samu nasara.
A gobe asabar idan Allah ya kaimu ake sa ran matashin zai tashi daga Kankia zuwa garin Tsanyawa ta jihar Kano, a garin Tsanyawa zai samu tarba daga shugabannin jam’iyyar  Apc na karamar hukumar Tsanyawa, bayan sun gaisa zai wuce karamar hukumar Bichi da ke cikin jihar Kano, inda zai yada zango a  Garin Bichi.
Haka kuma ana sa ran cewa Nura Aliyu Batsari zai samu tarba daga shugabannin jam’iyyar Apc na karamar hukumar Bichi, sannan zai kai gaisuwa ga Mai Martaba Sarkin Bichi Alhaji Aminu Ado Bayero.
Kazalika idan Allah ya kaimu lahadi da safe  zai wuce zuwa cikin garin Kano fadar Gwamnatin jihar Kano, inda zai sadu Mai girma Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya gabatar da jawabin shi na taya murna.
Wannan tattaki dai kamar yadda ya fada, yana a matsayin girmamawa ne daga ‘ya ‘yan jam’iyyar APC ta jihar Katsina zuwa ga gwamna Abdullahi Umar Ganduje da kuma al’ummar jihar Kano baki daya

Kai duniya ina zaki damu!!an tsinci gawar wai almajiri abirnin kano

Al’ummar unguwar Dorayi karama sun kama wani mutum mai suna Musa da ya jefar da gawar wani almajiri
- Al’amarin ya faru ne yammacin jiya Laraba amma sai wata mata mai suna Amina ta hango shi ta Katanga

- Matasan unguwar ne basu aminta da abinda mutumin ya aje ba, hakan yasa suka yi tara-tara suka damke shi tare da mika wa ‘yan sanda
Al’ummar Unguwar Dorayi karama sun kama wani mutum mai suna Musa da ya jefar da gawar wani almajiri mai suna Nasir a yankin.
Lamarin ya faru ne da yammacin jiya Laraba, in da wata mata mai suna Amina ta hango shi ta Katanga a yayin da ya jefar da gawar. Ya yi wa matar barazanar cewa zai halakata, kamar yadda ta shaidawa gidan rediyon Dala.
Innalillahi: An tsinci gawar wani almajiri a Kano
Innalillahi: An tsinci gawar wani almajiri a Kano
Wasu shaidun ganau ba jiyau ba sun tabbatar wa da gidan rediyon Dala FM cewa sun ga gawar almajirin an rufe ta a cikin wani abu, da alama kuma har ta fara sauya kamanni. Ganin basu aminta da abinda aka ajiye din bane yasa suka yi tara-tara suka damke mutumin da ya ajeta.
Rahotanni daga unguwar na cewa wanda aka kashe din wani almajiri ne mai suna Nasiru wanda aka dau tsawon kwanaki biyar kenan malamin sa na neman sa.
Hakazalika, al’ummar unguwar sun shaidawa Dala FM cewa ‘yan sanda sun cafke matashin da ya jefar da gawar tare da uwar dakin almajirin.
Sai dai har yanzu bamu samu jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano ba, sai dai zuwa nan gaba idan a